ABNA24 : A cikin watan Maris na shekara ta 2015 ne gwamnatin kasar Saudiya tare da kawayenta na kasashen larabawa suka farwa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasar Abdu Rabbu Mansur Hadi kan kujerar shugabancin kasar.
Yakin wanda kasashen Amurka da Turai suke goyon bayasa, a cikin shekaru 6 da suka gabata, sun sayarwa wadannan kasashen larabawa makamai masu yawa.
Har’ila yau MDD ta bayyana cewa fiye da rabin mutanen kasar suna rayuwa ne ta taimakon kungiyoyin bada agaji. An kashe mutane fiye da 100,000 sannan wasu da dama suka ji rauni a yayinda kasashen suka yiwa kasar kofar rago.
Sabuwar gwamnatin kasar Abuka dai ta ce zata matsawa kasashen laraba wa kawo karshen yakuin.
342/